Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Majiyar sojan Syria ta bayyana cewa da misalin karfe 6:45 na yammacin jiya ne yahudawan Isra'ila suka kai wani farmaki ta sama daga arewacin kasar Lebanon, inda suka nufi wasu wurare a yankin tsakiyar kasar.
Majiyar ta tabbatar da cewa, dakarun tsaron sama sun yi arangama da makamai masu linzami na Isra'ila tare da harbo wasu daga cikinsu.
Wannan dai na daga cikin ayyukan wuce gonad a iri da Isra’ila ke yi kan kasar Syria a cikin shekarun baya-bayan nan, ba tare da kasashen duniya sun uffan kan hakan ba.
342/